Labarai
Gwamnatin Ganduje ta magantu kan zargin Jam’iyyar NNPP
Gwamnatin jihar Kano ta musanta batun yin kafar ungulu wajen mika mulki ga sabuwar gwamnati, tana mai cewa, a shirye take domin miƙa mulkin cikin ruwan sanyi.
Gwamnatin ta bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ta fitar mai ɗauke da sa hannun kwamishinan yaɗa labarai Malam Muhammad Garba.
Sanarwar ta ce, tuni aka samar da babban kwamiti da kuma ƙanana da za su taimaka domin ganin an miƙa mulkin salin-alin.
Haka kuma Kwamishinan, ya musanta iƙirarin jam’iyyar NNPP da ke jiran karɓar mulki na cewa gwamnatin Ganduje na yi wa shirin miƙa mulki zagon ƙasa.
Ya kara da cewa, kwamitin miƙa mulki na ɓangaren gwamnatin Ganduje na rubuta rahoton ƙarshe kafin miƙa mulkin.
Muhammad Garba ya kuma bayyana cewa kamata ya yi kwamitin karɓar mulkin na gwamnati mai jiran gado shi ma ya shirya domin karɓar rahoton, wanda ya yi alƙawarin miƙawa a kan lokaci.
Kwamishinan ya kuma ce, kamata ya yi gwamnati mai jiran gado ta mayar da hankali game da shirin da take yi na karɓar mulki, ta kuma kiyaye duk wani abu da zai iya janyo fitina a yayin miƙawar.
You must be logged in to post a comment Login