Connect with us

Labarai

Gwamnatin Ghana ta kafa sabuwar doka don magance matsalolin tsaro

Published

on

Gwamnatin kasar Ghana ta kafa wata sabuwar doka da nufin magance matsalolin tsaro a yankin Tekun Gulf na Guinea.

 

Dokar wadda Majalisar Dokokin ƙasar ta amince da ita, za ta taimaka wajen yaƙi da fashin teku, fashi da makami a ruwa da sauran laifukan da ke barazana ga harkokin jiragen ruwa.

 

Hukumar Kula da Harkokin Teku ta Ghana ta ce ta yi aiki tare da Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya mai yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi da Laifuka da Tarayyar Turai domin wayar da kan hukumomin tsaro kan yadda za a aiwatar da sabuwar dokar.

 

Mataimakin darakta janar na hukumar, Mubarick Masawudu, ya bayyana dokar a matsayin wani babban mataki na daƙile ayyukan masu laifi da ke kawo cikas ga harkokin sufurin teku.

 

Sai dai masana sun yi gargaɗin cewa doka kaɗai ba za ta wadatar wajen kare yankin ruwan Ghana ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!