Labarai
Gwamnatin Kano ta sha alwashin dakile sayar da filayen ta ba bisa ka’ida ba

Gwamnatin Jihar Kano ta ce za ta ci gaba da daukar matakan dakile sayar da filayen gwamnati ba bisa ka’ida ba, tare da samar da gidaje da muhallai ga masu karamin karfi.
Kwamishinan Ma’aikatar Kasa da Tsare Birane ta Jihar Kano, Abduljabbar Muhammad Umar, ne ya bayyana hakan yayin bikin rabon takardun mallakar filaye ga mutane dubu daya daga kananan hukumomi 44 na jihar.
Kwamishinan ya ce an ware filayen ne domin samar da muhalli ga masu karamin karfi, inda aka tanade su da muhimman abubuwan more rayuwa.
Ya kuma bukaci wadanda suka amfana da filayen da su rike su domin amfanin kansu da iyalansu, tare da gujewa sayar da su domin biyan bukatun yau da kullum.
A cewarsa, tuni gwamnatin jihar ta sanya dokar ta-baci kan masu raba filaye ta hanyar awo da igiya, da kuma wadanda ke sayar da filayen gwamnatin jihar ba bisa ka’ida ba.
You must be logged in to post a comment Login