Connect with us

Labarai

Adadin yan ta’adda da ke mika wuya Arewa maso Gabas ya ƙaru- Rundunar Soji

Published

on

Rundunar sojin Najeriya, ta ce, adadin ‘yan ta’adda da abokan hulɗarsu da suka mika wuya ga dakarunta a yankin Arewa maso Gabas ya ƙaru da kashi 213 a cikin mako guda.

Rundunar ta ce hakan na faruwa ne sakamakon ci gaba da ayyukan soji na Operation Hadin Kai, da nufin rage ƙarfin ‘yan ta’addan da kuma katse hanyoyin samar musu da kayayyaki.

Jami’in yaɗa labarai na rundunar haɗin gwiwa ta rundunar a Arewa maso Gabas, Kyaftin Mohammed Goni, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

A wani ci gaban kuma, wasu manyan mambobin ƙungiyar ta’addancin guda biyu sun mika wuya ga sojoji tare da miƙa makamai da alburusai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!