Kiwon Lafiya
Gwamnatin Gombe ta koka kan yadda ake aikata laifukan fyade
Gwamnatin Jihar Gombe ta koka kan yadda aikata laifukan fyade suka zamo ruwan dare game Duniya a Jihar musamman ma a kwanakin nan.
Gwamnan Jihar Gombe Ibrahim Dankwambo ne ya shaida hakan lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar Lauyoyi Mata ta Duniya FIDA reshen Jihar Gombe a Ofishinsa, a wani bangare na bikin makon FIDA na bana.
Dankwambo ya ce an samu rahoton aikata laifin fyade bayan ko wane kwanaki biyu cikin makonnin ukun da suka gabata, kuma al’amari da gwamnati ita kadai ba za ta iya magance shi ba har sai an samu hadin gwiwa da kungiyoyi irin na su da kuma al’umma.
Haka zalika gwamnan ya ce ya umarci jami’an tsaro su tsaurara tsaron a Makarantun kwana na Mata a fadin Jihar domin karfafawa iyayen yara wajen kai ‘ya’yayensu Makaranta.
A na ta bangaren shugabar kungiyar ta FIDA reshen Jihar Gombe Sa’adatu Ishaya, ta nuna damuwarta kan gurbacewar al’umma da ta kai jallin cewa aikata laifukan fyade da kuma shaye-shaye tsakanin kananan yara da mata da ma matasa sun zama ruwan dare game Duniya.
Sannan ta yi kira ga hukumomi da su tabbatar da katange dukkanin Makarantun Mata da ba su da katanta