Labarai
Gwamnatin Jihar Filato ta bayar da umarnin sake bude Makarantu

Gwamnatin Jihar Filato ta bayar da umarnin sake bude dukkan makarantun firamare da sakandare na gwamnati da masu zaman kansu a faɗin jihar.
Gwamnatin ta rufe makarantun ne na dan lokaci, sakamakon rahotannin samun wadanda ake zargin sun kamu da cutar mashako wato Diphtheria a jihar.
Kwamishinar yada Labarai ta jihar, Joyce Lohya Ramnap, ta ce za a koma makarantu daga ranar Litinin 14 ga Satumba, 2026.
An dai rufe makarantun ne tun ranar 7 ga Satumba, domin bai wa hukumomin lafiya damar tantance halin da ake ciki tare da ƙarfafa matakan kariya daga yaɗuwar cutar.
Gwamnatin ta umarci shugabannin makarantu da su tabbatar da tsaftar muhalli, tare da sa ido kan duk wata alama da za ta iya nuna cewa ɗalibi ko ma’aikaci ya kamu da cutar.
Haka kuma, ta buƙaci iyaye da masu kula da yara da su kula da tsafta, tare da kai duk wanda ake zargin ya kamu da cutar zuwa cibiyar lafiya domin a duba shi.
Gwamnatin ta kuma yi gargadin cewa bai kamata a rika bai wa wanda ake zargin ya kamu da cutar magani ba tare da shawarar ma’aikacin lafiya ba.
You must be logged in to post a comment Login