Connect with us

Labarai

An rufe dukkan makarantun firamare da sakandare a Filato

Published

on

Gwamnatin Jihar Plateau ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun firamare da sakandare na jihar na wani dan lokaci, domin dakile yaduwar cutar mashako wato diphtheria.

 

Gwamna jihar Caleb Mutfwang ne ya bayar da umarnin, wanda zai fara aiki daga Litinin, 7 ga Satumba, 2026, kuma zai ci gaba har sai an ba da wani sabon umarni.

 

Rahotanni sun ce mutane 23 sun mutu sakamakon cutar a jihar, yayin da aka samu mutane 148 da ake zargin sun kamu da ita. 

 

A halin yanzu, marasa lafiya takwas na jinya a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH), yayin da wasu biyar ke kwance a asibiti.

 

Kwamishinan lafiya na jihar, ya ce gwamnati ta sanar da cibiyar dakile cutuka masu yaduwa NCDC tare da karbar kayan aikin da ake bukata domin tattara samfura da aika su dakin gwaje-gwaje.

 

Ya bukaci iyaye su tabbatar da cewa ‘ya’yansu sun kammala allurar rigakafin diphtheria, tare da neman agajin likita cikin gaggawa idan yara suka fara nuna alamun cutar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!