Labarai
Gwamnonin jihohin Arewa sun yi alhinin rasuwar Bamanga Tukur

Gwamnonin jihohin Arewa karkashin ƙungiyar Northern States Governors’ Forum, sun yi alhinin rasuwar tsohon gwamnan tsohuwar jihar Gongola kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Bamanga Tukur.
Shugaban ƙungiyar kuma gwamnan Gombe, Muhammadu Yahaya, ya bayyana rasuwar Tukur a matsayin babban rashi ga Arewa da Najeriya. Tukur, wanda aka fi sani da Tafidan Adamawa, ya rasu a Abuja ranar Asabar.
Gwamna Yahaya ya ce Bamanga Tukur ya shafe sama da shekaru sittin yana hidimar Najeriya, inda ya riƙe manyan mukamai ciki har da shugaban Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya, gwamnan tsohuwar jihar Gongola da kuma ministan Masana’antu.
Ya kuma yaba da gudunmawar da marigayin ya bayar wajen bunƙasa tattalin arzikin Afirka da harkokin siyasa, musamman lokacin da yake shugaban jam’iyyar PDP daga shekarar 2012 zuwa 2014. Ya yi addu’ar Allah Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya saka masa da alheri kan hidimar da ya yi wa ƙasa, Ya kuma shigar da shi Aljanna.
You must be logged in to post a comment Login