Labarai
Gwamnatin Jihar Gwambe tayi kan matakin Gwamnatin tarayya
Gwamnatin jihar Gombe ta bayyana rashin jin dadin ta kan matakin gwamnatin tarayya na dakatar da shirin samar da wuraren kiwo da kuma tsugunar da makiyaya a wasu jihohin kasar nan.
Gwamnan jihar Alhaji Inuwa Yahaya ne bayyana hakan lokacin da yake ganawar da manema labarai, jim kadan bayan wata ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Villa da ke Abuja.
Gwamnan jihar ta Gombe ya lura da cewa jihar sa tana da Hekta sama da dubu dari biyu da suka shirya bawa gwamnatin tarayya a matsayin tasu gudun mowar don ganin an samu nasarar cimma abinda aka sanya a gaba kan shirin.
A cewar sa akwai manoma da makiyaya da suke bukatar tallafi, musamman wadanda rikice-rikice ya dai-dai ta da har yanzu basu gama farfadowa ba, sai dai yana ganin shirin zai taimaka wajen rage musu radadin da suke fama da shi na asarar da suka tafka a baya.
Gwamna Alhaji Inuwa Yahaya na jihar ta Gombe ya bayyana cewa matsawar aka karbi shirin samar da wuraren kiwon ga makiyaya, shakka hakan zai taikama wajen inganta rayuwar su