Labarai
Gwamnatin jihar Jigawa ta fara biyan ‘yan Fansho
Gwamnatin jihar Jigawa ta fara biyan yan fansho su kimanin 570 sama da naira biliyan daya.
An raba mutanen zuwa rukuni-rukuni saboda kaucewa cunkoson don rage yaduwar corona da ke yiwa duniya barazana a halin yanzu.
Shugaban hukumar fansho ta jihar Jigawa, Alhaji Hashimu Ahmad Fagam ne ya bayyana haka a jiya Talata lokacin da yake bayyana irin ayyukan hukumar fansho a jihar ta Jigawa.
Alhaji Hashimu Ahmad Fagam ya ce tsofaffin ma’aikatan da za su ci gajiyar shirin sun hada da wadanda suka fito daga jihar da kananan hukumomi a matakin farko.
Ya kuma ja hankalin tsofaffin ma’aikatan da suka samu hakkokin su da su yi amfani da su ta hanyar da ta dace.
Shugaban ya kuma ce wadanda suka rasu da kuma sauran balas na wadanda suka yi ritaya za a biya kudin a matakin da ake ciki.
You must be logged in to post a comment Login