ilimi
Gwamnatin jihar Kano ta alƙawarta baiwa daliban lafiya aiki guda 146
Gwamnatin jihar Kano ta alƙawarta bai wa ɗaliban da suka kammala karatu a sashin nazarin kimiyya da harhaɗa magunguna aikin yi.
Gwamnatin ta yiwa ɗaliban jami’ar Bayero da ke karantar sashin harhaɗa magunguna Waɗanda za su kammala a bana alƙawarin.
Babban darakta a hukumar kula da Asibitoci na jihar kano Dakta Nasiru Alhassan Kabo ne ya bayyana hakan yayin taron bikin yaye daliban da suka kammala karatunsu a sashen.
Dakta Nasiru Kabo ya ce “Wannan wani ɓangare ne na ganin an bunƙasa harkokin kiwon lafiya a jihar kano”.
“Gwamnati za ta ci gaba da bai wa dukkanin waɗanda suka dace guraban aiki musamman a fannin lafiya” in ji Dakta Nasiru Kabo.
Jami’ar ta yaye ɗalibai 146 waɗanda suka kammala karatun su a fannin nazarin kimiyyar harhaɗa magunguna.
You must be logged in to post a comment Login