Labarai
Gwamnatin jihar Kano ta bada umarnin bude asibitin UMC Zhahir
Gwamnatin Jihar Kano ta ba da umarnin sake bude asibitocin UMC Zhair da ke Janbulo bayan rufewar da aka yi na tsawon wata guda, bisa zargin su da ajiye mai dauke da cutar COVID-19.
Tun da fari dai gwamnatin Jihar ta ba da umarnin rufe asibitin, saboda karya dokokin COVID-19 tun a ranar 2 ga watan Fabrairun da ya gabata.
A cewar gwamnatin jihar Kano asibitin ya karya doka ta hanyar kin tura mara lafiyar da ake zargin ya kamu da cutar corona zuwa cibiyoyin da aka ware domin kebe su, matakin da ya sabawa kwamitin kar-ta-kwana mai yaki da cutar a nan Kano.
Sai dai kuma umurnin sake budewar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren zartarwa na hukumar kula da cibiyoyin kiwon Lafiya Dakta Usman Tijjani Aliyu ya fitar a daren jiya Alhamis.
A cewar sanarwar, bayan sake duba Asibitin da aka yi kwamishinan Lafiya Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ya gamsu da matakin da asibitin ya dauka don kare faruwar hakan a gaba, a don haka asibitin zai ci gaba da ayyukan sa daga yau Juma’a.
You must be logged in to post a comment Login