Labarai
Gwamnatin jihar Kano ta musanta zargin sauya wa ‘yan fansho tsarin karbar fansho
Gwamnatin Jihar Kano ta mussanta zargin da ake yadawa cewa tana shirin sauya wa ‘yan fansho na jihar nan tsarin karbar fansho zuwa kamfanoni masu zaman kan su.
Shugaban ma’aikata na jihar Kano Alhaji Muhammad Auwal Na Iya ne ya bayyana hakan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan freedom radiyo daya mayar da hankali kan biyan ‘yan fensho hakokin su, da ya gudana da safiyar yau.
Muhammad Auwal Na-Iya yace gwamnati mai ci ta gaji bashin ‘yan fansho daga gwamnatin da ta gada ,yayin da a hanlin yanzu ta biya ‘yan fasnhon Ffiye da Naira biliyan 2 lakadan.
Shugaban ma’aikatan ya kara da cewar saboda muhimmancin da ‘yan fasnho ke da shi a cikin al’umma take kokarin ganin ta cigaba da sauke hakokin da ya rataya a wuyan ta wajen biyan su dukkanin basukan da suke bi.
Malam Auwal Na-Iya ya kara da cewar sun fito da tsarin taimakekeniyar lafiya ne domin kula da halin da ma’aikata suka shiga yayin da iyalan su basu da lafiya,akan haka ne ya sake nanata cewa ma’aikatan da ba su yi rijita ba da su gaggauta zuwa asibitoci don yin rijista.
Shugaban ma’aikatan na jihar Kano yace kimanin Naira biliyan daya da miliyan dari uku gwamnati ke biyan ‘yan fansho hakokin su a duk wata dake jihar nan, don saukake musu wahalhalun su.