Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin Jihar Kano Za ta Kashe Sama da Biliyan 2 domin gudanar da wasu ayyuka

Published

on

Kwamishinan yaɗa labaran Jihar Kano Baba Halilu Ɗan tiye ya bayyana hakan a yau 30 ga watan Nuwamba 2023 a zaman majalisar zartarwa na 9

Yayin da yake jawabi ga manema labarai kan abubuwan da majalisar zartarwar jihar Kano ta sahale domin kashewa a fannoni daban daban na ma’aikatun gwamnatin kano

Gwamnatin ta ce zata kashe miliyan 96,999,925.21 domin siyan kayan aiki a wajen kula da masu ciwo mai tsanani ICU na Asibitin Murtala.

Sai Kuɗi naira miliyan 69,803,903.68 domin gyara titin Muhammad Buhari Road dake kabuga zuwa kofar Ruwa.

An ware naira Miliyan 220,229,000.00 domin siyan motoci 3 na bayar da agajin gaggawa.

Haka kuma an ware miliyan 370,433,099.98 domin gina ɗakin taro da masallacin mata a hukumar Hisbah dake sharaɗa.

An ware kuɗi naira miliyan 41,586,723.66 domin gyara na hukumar da ke kula da dokoki da gyare-gyaren sa.

An ware miliyan 190,077,413.65 domin gina gidaje guda 8 masu ɗaki 2 da kuma gidajen masu gadi katangu na gidan gwamnati.

An ware miliyan 191,974,918.25 domin gina cibiyar koyar da aiki ɗaɓ’i a kano printing press.

Akwai kudi naura miliyan 23,999,139.41 gyare-gyaren gidan gwamnatin Kano dake birnin tarayya Abuja.

Haka kuma an ware Miliyan 107,383,775.50 domin gyara wasu gine-gine a ma’aikatar kimiyya da fasaha ta jihar Kano.

An ware miliyan 212,731,153.67 domin gyara asibitin Muhammad Abdullahi Wase.

An ware naira miliyan 54,802,333.11 domin gyara makarantar koyon aikin kiwo dake Bagauda.

Za’a kashe kuɗi naira miliyan 582,045,348.28 domin gyara titin Bayero Soli wanda ya haɗu da titin Zoo Road da ya biyo ta bayan Ado Bayero Mall.

Da kuma gyaran wata babbar fada da ta lalace Fajewa Kayarda Birnin Bako Road a ƙaramar hukumar Takai.

Jimillar kudin sun kama 2,343,137,320.51

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!