Manyan Labarai
Gwamnatin jihar Kano zata hana ‘’Yan kasa da shekaru 18 shiga Otel
Gwamnatin Jihar Kano tace zata hana yan kasa da shekaru goma sha takwas shiga Otel.
Manajan daraktan hukumar kula da yawan shakatawa ta jihar Kano Yusuf Lajawa ne ya bayyana hakan a tattaunawar da yayi da shirin Barka da Hantsi na nan Freedom Radio.
Yusuf Lajawa yace baza su amince yara ‘’yan kasa da shekaru sha takwas a Duniya na ta’ammalli a Otel ba sai dai da iyayansu.
Yace tsarin dokar ta hana yara ‘’yan kasa da shekaru goma sha takwas shiga otel zai fara aiki ne a shekarar bana ta 2020.
Da dumi-dumi: Hisbah ta janye dokar hana cakuda maza da mata
Hisbah bata da hurumin yin bulala ko cin tara ga mai laifi -Barista Sunusi Musa
Lajawa yace tun sanda ya karbi ragamar shugabancin hukumar ta yawon bude ido ta Jihar Kano ya kulla alaka mai karfi da jami’an tsaro na kowanne fanni domin samun nasarar ayyukan sa.
Ya kara da cewa daga karfe goma sha biyu na dare dole duk wasu guraran bukukuwa su dakatar da ayyukan su da ya hada da cibiyoyin yin biki.
Sannan ya bukaci al’ummar jihar Kano da su bashi hadin kai dan gudanar da ayyuka yadda ya kamata.