Connect with us

Labarai

Sarkin Zazzau ya kai ziyarar jaje Maraban Jos bisa kisan Ummulkhairi

Published

on

Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ya jagoranci wasu daga cikin ‘yan Majalisar Masarautarsa zuwa Maraban Jos domin yi wa iyalan Marigayya Malama Ummulkhair ta’aziyya, wadda aka kashe a wani lamari mai tayar da hankali.

 

A cewar wata sanarwa da Sashen Yaɗa Labarai na Masarautar Zazzau ya fitar, Sarkin ya bayyana alhininsa da matuƙar jimaminsa kan wannan mummunan al’amari.

 

Ya kuma miƙa sakon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayiyar tare da kira gare su da su ɗauki wannan jarabawa da haƙuri da kuma yarda da ƙaddarar Allah Maɗaukakin Sarki.

 

Hakazalika, Sarkin ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayiyar kura-kuranta, Ya kuma saka mata da Aljannatul Firdaus.

 

Mai Martaba Sarkin Zazzau ya kuma yi kira ga al’umma da su kwantar da hankalinsu su jira sakamakon bincike da matakan da gwamnati za ta ɗauka, tare da gujewa ɗaukar doka a hannu domin tabbatar da zaman lafiya da adalci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!