Labarai
Iran ta kai hare-hare kan sansanin sojin Amurka

Rundunar juyin juya halin Iran IRGC ta Iran ta sanar cewa da safiyar Lahadi ta kai hari kan muhimman wuraren sojojin Amurka a ƙasashen Kuwait da Bahrain, ta da makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuƙa.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce ta kai harin ne a wurare takwas na sojojin Amurka, ciki har da sansanin jiragen sama na Ali al-Salem Air Base da ke Kuwait, da kuma hedikwatar rundunar ruwa ta Amurka ta Fifth Fleet da ke Bahrain.
Rundunar ta IRGC ta ce wannan hari martani ne ga hare-haren da Amurka ta kai a baya.
Sai dai har yanzu jami’an Amurka ba su yi tsokaci ba kan girman ɓarnar da aka yi ko yiwuwar asarar rayuka.
Haka kuma IRGC ta zargi Amurka da kai hari kan sansanonin ruwan Iran guda biyar, tana mai cewa an yi hakan ne da sunan cewa rundunar ruwan IRGC ta tare wani jirgi.
Sanarwar ta jaddada cewa bisa yarjejeniyar da aka cimma, Iran ce ke da alhakin kula da zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz, kuma daga yanzu rundunar IRGC za ta ɗauki matakai masu tsauri kan duk wani jirgin ruwa da ta ɗauka a matsayin “mai karya doka.”
You must be logged in to post a comment Login