Connect with us

Kiwon Lafiya

Gwamnatin Kaduna ta gurfanar da mutane 65 bisa zarginsu haddasa rikici a kasuwar magani

Published

on

Akalla mutune 65 gwamnatin Jihar Kaduna ta gurfanar a gaban kotu bisa zarginsu da hannu wajen haddasa rikici a Kasuwar Magani da ke karamar hukumar Kajuru ranar 26 ga watan Fabarairun jiya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 12 tare da asarar dukiya mai tarin yawa.

Mataimaki na musamman ga gwamnan Jihar Kaduna kan harkokin yada labarai Samuel Aruwan ne ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai, inda ya ce kotun ta dage sauraron karar har zuwa ranar 15 ga watan Maris din nan da muke ciki.

Samuel Aruwan ya bayyana cewa gwamnatin ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an hukunta duk wadanda aka samu da hannu cikin tayar da hankalin al’umma a Jihar ta Kaduna, sannan kuma ya bukaci al’ummar su rika mutunta juna.

Haka zalika ya yi kira ga jama’ar Jihar su kaucewa biyewa masu ingiza tashin hankalin addini ko kabilanci, ko ma wani tunzuri makamancinsa, kasancewar kundin tsarin mulkin kasar nan ya baiwa ko wane dankasa ‘yan-cin zama a ko ina tare da yin addinin da ya ga dama.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!