Labarai
Gwamnatin Kano na baiwa sana’ar Kanikanci muhimmanci
Gwamnatin jihar Kano ta ce ta fara mayar da hankali kan bunkasa sana’ar Kanikanci ta hanyar tura matasa wurare daban-daban don daukar horo kan gyaran motoci wanda hakan zai taimaka wajen samawa matasa aikin yi a ciki da wajen jihar.
Mai baiwa gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje shawara kan harkokin kanikanci injiniya Idris Hassan ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da Freedom Radio.
Ya ce ganin irin muhimmanci da wannan sana’a ke da shi ya sanya gwamnatin jihar Kano ta tura matasa wasu manyan kamfanonin gyaran mota don samun horo na musamman kan sabbin dabarun aikin.
Ya kara da cewa yawanci matasa da ake turawa daukar irin wannan horo masu shaidar kammala Sakandare ne, saboda tsarin wannan horo ya nuna cewa dole sai wanda ya iya karatu da rubutu ne zai gane karatun.
Wakilinmu Shamsu Da’u Abdullahi rawaito Mai baiwa gwamnan Kano shawara kan harkokin kanikanci injiniya Idris Hassan na kira ga matasa da aka baiwa horon, musamman ma wadanda ake shirin yayewa da su yi kokari wajen gudanar da sana’ar su cikin gaskiya da rikon amana tare da amfani da tallafin da za a ba su ta hanyar da ta dace.