Labarai
Gwamnatin Kano ta amince da saka na’urar Solar da sayen kayayyakin aiki a manyan asibitoci uku

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da aiwatar da aikin saka na’urar Solar da kuma sayen sabbin kayayyakin aikin lafiya a Babban Asibitin Fagwalawa Cottage, Babban Asibitin Ajingi, da Babban Asibitin Doguwa.
A cewar Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Kano, aikin zai kasance karkashin kulawar Kano Health Trust Fund (KHETFUND), karkashin jagorancin Dr. Fatima Zaharaddeen, domin inganta ayyukan kiwon lafiya a fadin jihar.
Wannan mataki, kamar yadda hukumar ta bayyana, na daga cikin shirye-shiryen gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na farfaɗo da tsarin lafiya, inganta kayayyakin aiki, da tabbatar da cewa jama’a na samun kulawa ta gari a asibitoci.
Aikin saka na’utorin zai taimaka wajen samar da wutar lantarki ba tare da yankewa ba domin gudanar da ayyuka a sassan da suka shafi gaggawa, dakin haihuwa da na gwaje-gwaje. Haka kuma, sabbin kayayyakin aikin da za a saya za su taimaka wajen inganta bincike da jiyya ga marasa lafiya.
You must be logged in to post a comment Login