Labarai
Gwamnatin Kano ta amince da shirin wayar da kan Iyaye kan Tarbiyya

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da shirin wayar da kan iyaye game da muhimmancin kula da tarbiyyar ’ya’yansu, domin inganta ɗabi’u nagari tsakanin yara da matasa a jihar.
Shirin, wanda Sunusi Mu’azu, Babban Mai Ba da Rahoto na Musamman (SSR) ga Gwamnan Kano a Ma’aikatar Harkokin Addini ta Jihar Kano, zai jagoranta, zai yi amfani da gidajen rediyo da kafafen sada zumunta wajen isar da saƙonnin wayar da kai ga iyaye da sauran al’umma.
Shirin zai mayar da hankali kan nauyin da ke kan iyaye wajen renon ’ya’yansu bisa ladabi, biyayya, gaskiya da sauran kyawawan ɗabi’u, tare da jaddada muhimmancin sa ido kan abokan hulɗar yara da abubuwan da suke kallo ko sauraro a kafafen sadarwa na zamani.
Haka kuma, shirin zai ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin iyaye, malamai, shugabannin addinai da sauran masu ruwa da tsaki, domin magance matsalolin tarbiyya da samar da kyakkyawan yanayi ga yara da matasa.
You must be logged in to post a comment Login