Connect with us

Labarai

Tinubu ya bukaci kotun Amurka ta yi watsi da karar da ake masa

Published

on

Shugaba Tinubu

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya roki wata kotun tarayya a Amurka da ta yi watsi da sabon yunkurin wani  Dan Amurka mai fafutukar tabbatar da gaskiya, Aaron Greenspan, na shigar da karin takardu a wata shari’ar neman bayanan binciken hukumomin tsaro na FBI da DEA.

 

Takardar kin amincewar da lauyoyin Tinubu suka shigar tana dauke da ranar 15 ga watan Oktoban 2026, a gaban Kotun Tarayya ta Gundumar Columbia da ke Amurka.

 

Aaron Greenspan dai na neman a fitar masa da wasu takardu da suka shafi binciken da hukumomin Amurka suka gudanar kan Tinubu da wasu mutane a karshen shekarun 1980 zuwa farkon shekarar 1990, dangane da zargin da ya shafi harkokin miyagun ƙwayoyi.

 

Sai dai har yanzu ba a bayyana hukuncin da kotun za ta yanke kan wannan sabon yunkuri ba.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!