Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano ta bukaci ƴan takara da jam’iyyu su yi yakin neman zabe cikin gaskiya

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta yi kira ga dukkan ƴan takarar siyasa da jam’iyyun da za su fafata a zaɓuka masu zuwa da su gudanar da yakin neman zaɓensu cikin gaskiya, amana da mutunta juna.

 

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai, inda ya yi magana kan muhimmancin gudanar da harkokin siyasa cikin lumana da mutunta dokokin ƙasa.

 

Gwamnan wanda ya samu wakilci Daraktan Yaɗa Labaran sa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya ce siyasa bai kamata ta zama hanyar haifar da gaba, rikici ko rarrabuwar kan al’umma ba, yana mai cewa ƴan takara na da damar bayyana manufofinsu tare da barin al’umma su tantance wanda suka ga ya dace da jagoranci.

 

Ya ƙara da cewa ya zama wajibi magoya bayan jam’iyyu su guji kalaman batanci, cin zarafi da duk wani abu da zai iya haddasa tashin hankali kafin, lokacin da kuma bayan zaɓe.

 

Wannan kira na zuwa ne yayin da harkokin siyasa da shirye-shiryen zaɓukan shekarar 2027 ke ƙara ɗaukar sabon salo a faɗin Najeriya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!