Connect with us

Labarai

NUPRC ta yi barazanar soke lasisin masu zuba jari da suka gaza fara aiwatar da ayyukan da aka ba su

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta yi barazanar soke lasisin masu zuba jari da suka gaza fara aiwatar da ayyukan da aka ba su karkashin shirin tallata amfani da iskar gas da ake konawa.

Hukumar Kula da Harkokin hako Man Fetur ta Majeriya NUPRC, ce ta bayyana hakan, tana mai cewa za ta duba ayyukan masu lasisin bayan shekara guda, tare da daukar matakin soke lasisi idan aka samu rashin ci gaba mai ma’ana.

Shirin na sayar da iskar gas da ake kona wa ya kunshi wuraren kona gas guda 43, yayin da aka riga aka bai wa masu zuba jari wurare 27 domin bunkasa su da kuma mayar da iskar gas din abin da za a iya amfani da shi wajen samar da makamashi da kuma samun kudaden shiga.

A shekarar 2025, hukumar ta ce ta tara sama da Naira biliyan 521 daga tarar da kamfanonin mai ke biya saboda kona iskar gas, Sai dai duk da tarar, har yanzu ana ci gaba da kona dimbin iskar gas, lamarin da ke janyo asarar albarkatu tare da haifar da matsalolin muhalli da lafiya ga al’ummomin da ke yankunan mai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!