Labarai
’Yan bindiga sun kashe mutum tare da sace ma’aikacin INEC a Sokoto

’Yan bindiga sun kashe mutum tare da sace ma’aikacin INEC a Sokoto
’Yan bindiga sun kai hari ƙauyen Girkau da ke Ƙaramar Hukumar Kebbe ta Jihar Sokoto, inda suka kashe mutum guda tare da yin garkuwa da wani ma’aikacin hukumar INEC.
Rahotanni sun bayyana sunan wanda aka kashe a matsayin Mallam Samaila Abdullahi Girkau, yayin da aka bayyana ma’aikacin INEC da aka sace a matsayin Bala Aladan.
Shaidun gani da ido sun ce maharan sun shiga ƙauyen suna harbe-harbe, kafin su tafi da waɗanda suka kama zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Rundunar ’yan sanda ta ce ta fara bincike tare da ƙara jami’an tsaro a yankin, yayin da ake ci gaba da aikin ceto waɗanda aka sace da kamo maharan.
You must be logged in to post a comment Login