Labarai
Gwamnatin Kano ta bukaci gwamnatin tarayya ta biya ta kudaden rarar Iskar Gas
Gwamnatin jihar Kano ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta sakar mata kasonta na rarar kudade daga tsarin iskar Gas na kasa NLNG na tsawon shekaru 25 da suka gabata.
Hakan na kunshe a cikin wata wasika da Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya aika wa shugaban majalisar dokokin Kano, Alhaji Jibril Ismail Falgore, inda ya bukaci majalisar kan ta shiga tsakani domin saukaka karbo rarar kudaden wanda hakkin jihar Kano ne tun daga watan Janairun 1999 zuwa yanzu.
Ta cikin wasikar, wadda kakakin majalisar ya karanta a zauren majalisar a zamanta na jiya Talata, gwamnan ya ce, in majalisar ta amince da kudurin, zai saukaka nemo masalaha don bin hanyoyin da suka dace domin karbo kudaden da aka tara na tsawon shekaru.
Da yake mayar da martani kan wasikar, shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Husseini, ya jaddada cewa kudurin majalisar shi ne hanyoyin samun kudaden, yana mai bayyana cewa, hakan zai bai wa kungiyar gwamnoni damar daukar shawarwarin da suka dace domin amso kudaden, zuwa jihohi.
You must be logged in to post a comment Login