Kiwon Lafiya
Gwamnatin Kano ta ce ta biya wa dalibanta su 335 kudin makaranta a jami’ar Al-Mansura
Gwamnatin jihar Kano ta ce ta biya kudin karatu ga wasu dalibai ‘yan asalin jihar Kano guda dari da talatin da biyar da ke karatun jinya a jami’ar Al-Mansura da ke kasar Masar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun hukumar Lawan Ibrahim Fagge.
Sanarwar ta ce babbar Sakatariyar hukumar Farfesa Fatima Muhammed Umar ce ta bayyana haka yayin da take zantawa da shugabannin kungiyar iyayen yara wato PTA reshen jami’ar ta Al-Mansura wadanda suka kai mata ziyara.
Cikin sanarwar dai babbar Sakatariyar ta ce gwamnati ta kashe naira miliyan dari da goma sha biyu da dubu dari tara da arba’in da takwas da dari biyu wajen biyan kudaden karatu ga daliban.
Babbar Sakatariyar hukumar ta cikin sanarwar dai ta ce ko da dalibai talatin da bakwai da gwamnati ta dakatar da biyan musu kudin tallafin karatu saboda rashin samun sakamako mai kyau, su ma sun ci gajiyar tallafin kudaden abinci da na wajen kwana na watanni bakwai-bakwai.