Labarai
Gwamnatin Kano ta dakatar da Shugaban Kwalejin Lafiya da shugaban hukumar kura Sakandire
Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da Shugaban Kwalejin Lafiya ta Health Technology Dakta Bello Ɗalhatu, da mai riƙon shugabancin Hukumar lura da makarantun Sakandire ta jihar Malam Ado Tumfafi.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da ofishin Sakataren gwamnati Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya fitar.
Sanarwar ta ce, an dakatar da su ne saboda zargin karɓar kuɗaɗe daga ɗalibai da kuma wasu ƙarin zarge-zarge.
Sanarwar ta zargi Tumfafi da karɓar kuɗin ɗalibai da sanya wa malamai harajin ba gaira ba dalili da sunan kuɗin fom ɗin ƙarin girma da sauransu.
Gwamnatin ta kuma umarci manyan sakatarori na ma’aikatun ilimi da lafiya da su kafa kwamitin bincike a kan mutane biyun.
Gwamnatin Kano ta kuma ce, ba za ta sassauta wa duk wani shugaban hukuma da ya yi amfani da ofishinsa wajen cuzguna wa jama’a ba.
Haka kuma ta yi alƙawarin ƙwato wa iyayen ɗalibai da Malamai da aka karɓi kuɗinsu.
You must be logged in to post a comment Login