Labarai
Gwamnatin Kano ta fara nazari kan takardar musanta naɗin Ganduje a Farfesa
Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce, yana nazarin takardar da jami’ar East Carolina (ECU) ta fitar wadda ta musanta ba shi matsayin Farfesa.
Mai bai wa gwamnan shawara kan yaɗa labarai Salihu Tanko Yakasai ne ya bayyana hakan ga Freedom Radio.
Yakasai ya ce, jami’ar ce ta aike wa gwamnan takardar naɗinsa a Farfesa da kuma ɗaukar aiki.
Jami’ar ta kuma sanya suna da hoton Gwamnan cikin malamanta, har ma ta wallafa hakan a babban shafinta na intanet inji Salihu.
Labarai masu alaka:
Ana kace-nace kan matsayin ‘Farfesa’ ga Ganduje
Siyasar Kano: PDP ta gargaɗi Ganduje kan cefanar da kadarorin gwamnati
Jaridar Premium Times ce dai ta samu wasiƙar musanta naɗin Gandujen a ranar Juma’a.
Jami’ar ta ce jami’inta ne ziƙau ya rubutawa Ganduje takardar naɗin, ba tare da ta samu amincewar hukumar jami’ar ba.
Sai dai Yakasai ya ce, yanzu haka gwamnati ta shiga nazarin takardar domin ɗaukar matakin da ya dace.
A ranar 1 ga Disamba ne sakataren yaɗa labaran gwamnan Malam Abba Anwar ya sanar da cewa an naɗa Ganduje Farfesa tare da ba shi aikin koyarwa a jami’ar.
You must be logged in to post a comment Login