Labarai
Gwamnatin Kano ta gyara madatsar ruwa ta Goron Dutse bayan shafe sama da shekaru 30 ba ta aiki

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da fara raba ruwa daga madatsar ruwa ta Goron Dutse, bayan shafe sama da shekaru 30 bata aiki.
Gwamnan ya kaddamar da aikin a ranar Litinin, 28 ga Satumba, 2026, inda ya bayyana farfaɗo da madatsar a matsayin wani babban ci gaba ga jihar Kano. Ya ce dawo da madatsar cikin aiki na daga cikin kokarin gwamnatinsa na farfaɗo da muhimman ababen more rayuwa da kuma magance matsalar karancin ruwan sha a jihar.
A nasa bangaren, Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi na jihar, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ya ce madatsar na da karfin ajiye ruwa kimanin lita miliyan 39 da dubu 800, inda a halin yanzu ake tura mata ruwa daga matatar ruwa ta Challawa domin rabawa al’ummomin sassa daban-daban na birnin Kano. Ya ce aikin wanda kamfanin CCECC ya gudanar, ya lakume kusan naira biliyan 11, kuma ya kunshi gyaran matatar Challawa da bututun da ke kai ruwa zuwa Goron Dutse, mai tsawon kilomita 15 da digo 6.
You must be logged in to post a comment Login