Labarai
Gwamnati za ta fara rarraba ruwa cikin mako guda a Kano

Gwamnatin jihar Kano ta ce ana sa ran za ta fara faɗaɗa rarraba ruwan sha ga al’ummomin jihar cikin mako guda, yayin da ake kammala aikin gyaran manyan cibiyoyin samar da ruwa.
Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi na jihar, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ya bayyana haka ne a shirin Barka da Hantsi na Nan Freedom Radio, inda ya ce ayyukan gyaran tashoshin sarrafa ruwa na Challawa da Tamburawa da kuma tafkunan Goron Dutse sun kusa kammala.
Ya ce ana kuma aikin dawo da layukan samar da ruwa, ciki har da layin kilomita 15.6 zuwa Goron Dutse, tare da gyaran fanfunan ruwa da na’urorin tace ruwa.
Dakta Hashim ya ce wasu daga cikin tsare-tsaren samar da ruwa na yankuna tara daga cikin 19 na jihar na kan aikin farfaɗowa, kuma wasu sun fara samar da ruwa bayan shafe shekaru suna aiki.
Kwamishinan ya ce gwamnatin na fuskantar gibin sama da lita miliyan 300 na ruwa a kowace rana a yankin Greater Kano, don haka ake kokarin magance matsalolin wutar lantarki, kayan aiki da kayayyakin more rayuwa. Ya kuma yi kira ga jama’a da su kare kayayyakin samar da ruwa tare da kai rahoton duk wani yunkurin lalata su ko yin haɗaɗɗiyar hanyar ruwa ba bisa ka’ida ba.
You must be logged in to post a comment Login