Connect with us

Labarai

SNB ta sake zaɓar Farfesa Umar Pate a matsayin shugabanta na ƙasa

Published

on

Ƙungiyar ma’aikatan kafafen yaɗa Labarai ta Najeriya watau SNB, ta sake zaɓar Farfesa Umar Pate a matsayin shugabanta na ƙasa, yayin da Alhaji Ado Saidu Warawa na nan Freedom Radio ya zama mataimakin shugaban ƙungiyar na shiyyar Arewa maso Yamma.

Haka kuma, an zaɓi Farida Abubakar, wadda ita ce mai kula da harkokin ƙungiyar ta SNB a jihar Kaduna, a matsayin ma’ajin kuɗin ƙungiyar ta ƙasa.

 

Farida Abubakar ita ce babbar daraktar sashen rediyo na Hukumar Yaɗa Labarai ta Jihar Kaduna KSMC.

 

An gudanar da zaɓen ne a yayin taron shekara-shekara na kungiyar karo na uku wanda aka gudanar a jihar Bauchi, tare da halartar mataimakin gwamnan jihar, Auwal Jatau, da shugaban ƙungiyar ‘yan jarida ta ƙasa, NUJ, Kwamared Alhassan Yahaya, da sauran masu ruwa da tsaki a harkar yaɗa labarai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!