Connect with us

Labarai

Gwamnan Kano ya kaddamar da sakin Ruwan Sha zuwa Kwaryar Birnin Kano

Published

on

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da sakin ruwan sha zuwa kwaryar birnin Kano, bayan kammala aikin gyaran ma’ajiyar ruwa ta saman Goron Dutse da aka yi domin inganta samar da ruwan sha ga al’ummar birnin.

 

Gwamnan ya kaddamar da sakin ruwan ne yayin ziyarar da ya kai ma’ajiyar ruwan, wadda ke dab da kammala aikin gyaran da aka gudanar a cikinta. Ma’ajiyar ruwan za ta riƙa tara ruwa tare da tura shi zuwa sassa daban-daban na kwaryar birnin Kano, inda ake sa ran za ta taimaka wajen inganta rarraba ruwan sha ga mazauna birnin.

 

Aikin gyaran ma’ajiyar ruwan ya ƙunshi inganta yadda ake tara ruwa da kuma tsarin tura shi zuwa cikin birni, inda adadin ruwan da ma’ajiyar za ta iya tarawa ya haura lita miliyan arba’in. Wannan na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ta ɗauka domin inganta samar da ruwan sha da rage matsalolin ƙarancin ruwa da al’ummar Kano ke fuskanta.

 

A nasa jawabin, Kwamishinan Ma’aikatar Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ya ce gwamnatin jihar ta samu nasarar kammala aikin gyaran ma’ajiyar ruwan a kan lokacin da ta yi alƙawari tun da farko.

Kwamishinan ya ƙara da cewa ma’aikatar za ta samar da lambobin wayoyin tarho na musamman da jama’a za su riƙa kira domin sanar da ita duk wata matsala da suka lura da ita dangane da samar da ruwan sha ko hanyoyin rarraba shi a cikin birnin.

Ya ce matakin samar da lambobin wayoyin zai taimaka wajen bai wa ma’aikatar damar samun bayanai kai tsaye daga jama’a tare da ɗaukar matakan gaggawa domin magance matsalolin da suka shafi samar da ruwan sha a sassa daban-daban na birnin Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!