Manyan Labarai
Gwamnatin Kano ta jadadda kudirin inganta kiwon lafiya
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya jadadda kudirinsa na tabattar da an inganta harkokin lafiya a wani yunkurin inganta harkokin kiwon lafiya a matakan daban-daban na jihar Kano
Mataimakin Gwamna Alhaji Nasir Gawuna ne ya bayyana hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki a harkarkokin lafiya da aka gudanar na kwanaki uku da ya gudana a nan Kano.
Ya ce taron dai an gabatar da shi ne a lokacin da ya dace , duba da yadda yawan al’umma ke karuwa hakan ne ya zama wajibi a tabbatar da an inganta harkokin lafiya yadda ya kamata.
Alhaji Yusuf Gawuna, ya kara da cewa tuni dai gwamnatin jihar Kano ta fara shirin tallafawa kiwon lafiya a matakin farko yayin da dubu dari uku da saba’in mutane 370,000 suka ci gajiyar wannan shiri.
Yace Shirin tuni aka inganta shi tare da fara aiki a hukumomin kiwon lafiya dari biyu da Arba’in da biyar da cibiyoyin lafiya dari da Talatin da Hudu sai manyan cibiyoyin lafiya Talatin da bakwai aka inganta su suka kuma suke aiki yadda kamata.
Mataimakin gwamnan Kano Alhaji Yusuf Gawuna ya ce gwamnatin dai har ila yau tuni ta fara aiwatar da shirin tara kudadden aiwatar da kiwon lafiya ga alummar jihar Kano, kamar yadda yake a kundin tsarin lafiya ta jihar Kano.