Labarai
Gwamnatin Kano ta kaddamar da shirin yashe magudanan ruwa domin kaucewa ambaliya

Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da shirin yashe magudanan ruwa a fadin jihar gabanin saukar daminar bana ta 2026.
Kwamishinan ma’aikatar Muhalli, Al’barkatun Ruwa da Sauyin Yanayi na jihar Kano Dr. Dahiru Muhammad Hashim ne ya jagoranci kaddamar da shirin a yankin Jakara da ke Karamar Hukumar birni a jihar Kano a ranar Al’hamis 04-6-2026.
Kwamishinan ya ce an bijiro da shirin yashe magudanan ruwan ne domin kaucewa ambaliyar ruwa a cikin unguwannin da ke kewaye da manyan kwatoci.
Haka zalika ya kara da cewa, gwamnati zata cigaba da gudanar da wannan aiki a fadin jihar Kano baki yada.
A karshen ya nemi hadin kan al’umma domin bayar da cikakken hadin kai a yayin gudanar da aikin.
You must be logged in to post a comment Login