Labarai
Adamawa: Mutane 6 sun rasu sakamakon hatsari tsakanin motar Sojoji da ta fasinja

Akalla mutane shida ne suka rasa rayukansu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da wata motar soji da kuma motar haya kirar Hummer a kan hanyar Girei zuwa Song a Jihar Adamawa.
Rahotanni sun ce hatsarin ya faru ne da misalin karfe 1:50 na rana ranar Laraba, inda motar haya da ke dauke da fasinjoji daga Yola zuwa Mubi ta yi karo da motar soji da ke kan hanyarta daga Gombi zuwa Yola.
Bayan afkuwar hadarin motar kirar Hummer ta kife tare da kamawa da wuta, lamarin da ya yi sanadin mutuwar dukkan fasinjojin da ke cikinta.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Adamawa, SP Suleiman Nguroje, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa daga cikin wadanda suka mutu akwai mambobi hudu na Hukumar Yi Wa Kasa Hidima ta Kasa (NYSC), wani soja da kuma wani mutum guda.
SP Suleiman Ya ce an kai gawarwakin mamatan zuwa Asibitin Kwararru na Yola, yayin da ake ci gaba da bincike da kuma kokarin gano sauran wadanda abin ya shafa tare da tuntubar iyalansu.
You must be logged in to post a comment Login