Labarai
Isra’ila da Lebanon sun amince da sake sabunta yarjejeniyar tsagaita wuta

Isra’ila da Lebanon sun amince da sake sabunta yarjejeniyar tsagaita wuta da ke tangal-tangal tare da samar da wuraren tsaro a kudancin lebanon.
Duk da a watan Afrilu sun cimma yarjejeniya, sai dai Isra’ila da Hezbollah na ci gaba da kai wa juna farmaki.
Lebanon ta ce fiye da mutane 3,300 ne aka kashe, yayin da wasu 10,000 suka jikkata tun bayan da sabon fada ya barke a tsakanin bangarorin biyu a watan Maris.
Karkashin yarjejeniyar da Amurka ke shiga tsakani, Hezbollah za ta janye daga wuraren da aka tsaurara tsaro a kudancin Lebanon.
Sai dai babu wani karin bayani kan wadannan wuraren da za a samar, wanda zai kasance karkashin ikon dakarun Lebanon.
A nata bangaren, Iran da ke goyon bayan kungiyar Hezbollah ta dage kan cewa, sai an dakatar da yakin Lebanon kafin duk wata yarjejeniyar zaman lafiya tsakaninta da Amurka.
You must be logged in to post a comment Login