Labarai
Gwamnatin Kano ta kama wani waje da ake ɓoye kayan tallafi kuma ake sauya musu buhu zuwa na siyarwa
Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da gano wani waje da ake zargin ana sauya buhunhunan kayan tallafin rage raɗaɗin da Gwamnatin ke rabawa ga al’umma A ƙalla Ƙananan buhunhuna sama da dubu guda aka samu inda ake zargin ana sauya musu buhu zuwa na sayar wa maimakon na kyauta
Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ne ya tabbatar da hakan yayin ziyarar gani da ido da ya kai wajen da yake a unguwar sharaɗa.
Da yake jawabi ga manema labarai Kwamishinan Noma Dan Juma Muhamud ya tabbatar da yadda gwamnatin ta tabbatar da kama kayan.
Sai dai Kwamishinan yace har yanzu ba’a san iya adadin buhuhunan da aka kama ba sai dai kawo yanzu ananan ana gudanar da bincike domin tabbatar da adadin su.
Sai dai yanzu an kama samu tsaron wajen da ake zargi tare da su aka haɗa baki domin ajiye kayan.
You must be logged in to post a comment Login