Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano ta musanta labarin hana Kwankwaso shiga jihar

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta musanta labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta wanda Alhaji Buba Galadima ya yada, cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rubuta wasika zuwa Gwamnatin Tarayya don hana Sanata Rabiu Musa Kwankwaso shiga jihar. 

 

A cikin sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya fitar, gwamnatin ta bayyana cewa wannan labari, na da nufin, yaudarar jama’a da tayar da rikici a siyasa.

 

Gwamnatin jihar ta kuma yi kira ga Alhaji Galadima da ya kawo hujja mai inganci ko ya janye wannan labari, yana mai tabbatarwa al’umma cewa babu wani rikicin siyasa da zai ja hankalin gwamnati daga aikin kawo ci gaba da kare hakkokin dimokuradiyyar duk ‘yan ƙasa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!