Labarai
Gwamnatin Kano ta raba kayan kula da lafiyar mata kyauta
Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudirin ta na cigaba da kula da lafiyar mata masu juna biyu da kananan yara ‘yan shekaru 5 zuwa kasa.
Sakataren hukumar kula da asibitoci na jihar Kano Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana hakan a yau, yayin rabon magunguna da kayan aikin lafiya na milyoyin Naira ga wasu asibitocin jihar nan.
Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ya ce gwamnatin jihar kano ta jima tana raba kayan ga manya da kananan asibitocin don saukaka wa al’umma a fannin kiwon lafiya.
Wasu daga cikin wadanda suka karbi kayan, da suka hada da Dahiru Haruna, wanda ke kula da magunguna na asibitin sha ka tafi na Dumbulun dake karamar hukumar Tsanyawa, da kuma wata ma’aikaciyar lafiya dake asibitin kwararru na Murtala, Iya Halliru Haruna, sun bayyana yadda suke yiwa marasa lafiya aiki da kayan.
Yayin rabon magunguna da kayayyakin, asibitin kwararru na Murtala ya amfana da magunguna da kayan aiki na sama da Miliyan 5.