Addini
Gwamnatin Kano ta sanar da Alhamis a matsayin ranar hutun shekarar Musulunci

Gwamnatin jihar Kano ta ayyana ranar Alhamis 26 ga watan Yunin bana a matsayin ranar hutu domin murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1447 bayan hijira.
Hakan na cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar a yammacin yau Laraba.
Sanarwar, ta ruwaito cewa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya taya al’ummar Musulmi murnar shiga sabuwar shekara da ta fara da watan Muharram, wata na farko a kalandar Musulunci.
Gwamnan ya yi kira ga al’ummar jihar da al’ummar Musulmi da su yi nazari bisa ayyukan da suka yi a shekarar da ta kare, sannan su yi amfani da wannan damar wajen gabatar da addu’o’in zaman lafiya da hadin kai da ci gaba a jihar Kano da ma kasa baki daya.
Haka kuma, ta cikin sanarwar, gwamnan, ya tabbatar wa al’ummar jihar kudurin gwamnatinsa na inganta rayuwar su ta hanyar gudanar da sadaukarwa da kuma tsarin ci gaban al’umma.
You must be logged in to post a comment Login