Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano ta sanar da ranar fara hutun karshen zangon karatu na biyu

Published

on

Gwamnatin jihar Kano, ta hannun Ma’aikatar Ilimi, ta sanar da ranar fara hutun karshen zangon karatu na biyu na kakar karatu ta 2025/2026.

 

A cewar sanarwar, dukkan makarantun firamare da sakandare na gwamnati da masu zaman kansu a fadin jihar za su tafi hutun zango na biyu daga ranar Juma’a 17 ga Afrilu, 2026 ga makarantun je ka ka dawo, da kuma ranar Asabar 18 ga Afrilu, 2026 ga makarantun kwana.

 

Sanarwar ta kuma bayyana cewa hutun zai bai wa dalibai da ma’aikata damar hutu da kuma shiri kafin fara zangon karatu na uku. Ana sa ran makarantu za su koma karatu a zango na uku ranar Lahadi 3 ga Mayu, 2026 ga makarantun kwana, da kuma Litinin 4 ga Mayu, 2026 ga makarantun je ka ka dawo, inda za a ci gaba da harkokin karatu kamar yadda aka tsara.

 

Kwamishinan Ilimi, Gwani Dakta Ali Haruna Abubakar Makoda, yayin da yake yi wa dalibai fatan alheri a lokacin hutun, ya shawarci iyaye da masu kula da yara da su tabbatar ‘ya’yansu sun koma makaranta a kan lokaci domin kauce wa tangardar karatu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!