Labarai
Kano: Kungiyar ma’aikatan shari’a ta janye yajin aikin da ta tsunduma

Kungiyar ma’aikatan Shari’a ta Najeriya reshen jihar Kano, ta bayyana janye yajin aikin da ta fara tsawon kwanaki uku biyo bayan amincewa da wasu bukatunsu da gwamnan Kano Alhaji Kabir Yusif ya yi.
Shugaban kungiyar Alhaji Abdullahi Aminu Shams ne ya bayyana hakan ga manema labarai kan matsayar da suka cimma.
Ya kuma godewa ma’aikatar yada labarai da ta Shari’a da kuma ta kula da ma’aikata kan yadda suka shiga cikin lamarin har ta kai ga sun cimma bukatun su.
Da ya ke jawabi kan cimma matsayar kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya ya bayyana cewar baya ga biyan hakkokin lauyoyin gwamnatin Kano ta kirkiro musu abubuwa na musamman da za su ciyar da su gaba.
You must be logged in to post a comment Login