Labarai
Gwamnatin Kano ta raba takardun Filaye ga masu Gidaje da Kangwaye da filaye a hanyar Lantarki

Gwamnatin Jihar Kano ta Mika takardun Filaye ga masu Gidaje da Kangwaye da filaye a karkashin Layin kamfanin dakon lantarki na TCN a unguwannin Sharada da Ja’en da kuma Rimin Zakara.
Da yake jawabi yayin rabon a yau Laraba, a madadin Gwamna, Kwmishinan ma’aikatar bibiyar ayyukan da Gwamnatin Kano ke gudanarwa Nura Iro Ma’aji, ya ce, gwamnatin ta kuma ware Fiye da naira Biliyan Bakwai domin biyan diyya ga mutanen da lamarin ya shafa.
A nasa jawabin Kowishinan ma’aikatar Kasa da tsare-tsare ta Jihar Kano Abduljabbar Muhammad Umar, cewa ya yi za su tabbatar da ganin kowanne mutum ya samu hakkinsa yadda ya kamata.
Mutanen da aka raba wa takardun filayen wadanda su ka hadar da Maza da Mata sun nuna jin dadinsu.
You must be logged in to post a comment Login