Labaran Kano
Gwamnatin Kano ta siyo kayayyakin yada Da’awa
Gwamnatin Kano ta siyo kayayyakin da za’a yi amfani da su wajan yada Da’awa a lungu da sako na jihar nan .
Babban daraktan hukumar dake yada Da’awa ta jihar Kano Malam Murtala Muhammad Adam ne ya bayyana hakan a yayin tattaunawa da Freedom Radio a nan Kano
Malam Murtala Muhammad Adam ya ce lokaci yayi da za’a yi amfani da kayayyakin don yada Da’awa a cikin birnin Kano.
Ya ce sun rarraba kayan ne ga kungiyoyin addinin musulunci da suka hada motoci da Amsa kuwa da dai sauran su.