Labarai
NECO ta ce Gwamnatin Kano ta biya ta bashin Miliyan 475

Hukumar shirya jarrabawar kammala makarantun Sakandare ta kasa NECO, ta tabbatar da cewar gwamnatin jihar Kano ta biyata basukan da suke binta na kudi da suka tasamman sama da naira miliyan dari hudu da Hamsin da Bakwai.
Shugaban hukumar a nan Kano Muhammad Abubakar Musawa ne ya bayyana hakan a zantawar sa da Freedom Radio dangane da bashin da gwamnati ta biya.
Ya kuma ce, duk a gwamnonin Najeriya babu gwamnatin da take biyan hakkokin daliban ta a hukumar kamar gwamnatin Kano.
Shugaban hukumar talNECO ya kuma yabawa hukumar kula da harkokin Karatu ta KERD karkashin jagorancin Hajiya Rabi Inuwa Hussain bisa jajir cewarta wajen ganin ilimi ya inganta a Kano.
You must be logged in to post a comment Login