Labarai
Gwamnatin Kano ta yi martani game da ƙorafin Ja’afar Ja’afar kan Ganduje
Gwamnatin Kano ta yi martani game da ƙorafin na Ja’afar Ja’afar.
Bayan da Freedom Radio ta tuntuɓe shi game da lamarin Kwamishinan yaɗa labarai na Kano Malam Muhammad Garba ya ce, ko kaɗan kalaman Gwamnan ba sa nufin afka wa Ja’afar ballantana a yi masa wata illa.
Kwamishinan ya ce, yanzu haka maganar tana gaban kotu, a saboda babu buƙatar yin dogon bayani a kai, da ka iya zamo wa raini ga kotu.
Muhammad Garba, ya ci gaba da cewa, kalaman Gwamna Gandune na nufin cewa zai ci gaba da ɗaukar mataki na shari’a a kan lamarin.
Tun da fari dai mawallafin jaridar DAILY NIGERIAN, Ja’afar Ja’afar, ya kai ƙara ga Sufeto-Janar na ƴan sandan ƙasar nan Mohammed Adamu.
Ja’afar na ƙorafin cewar, Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Ganduje ne ke da alhaki idan wani abu ya same shi.
Ƙorafin ɗan jaridar dai ya biyo bayan wasu kalaman Gwamnan a cikin wani shiri mai suna “A Faɗa A Cika” na sashen Hausa na BBC, da ya ce, suna shirye-shirye kuma za su ɗauki mataki a kan masu hannu cikin sakin bidiyon.
A watan Oktoban shekarar 2018 ne, jaridar DAILY NIGERIAN ta wallafa wasu faya-fayen bidiyo da ke nuna yadda gwamnan ke sanya daloli a aljihunsa, batun da ya ɗauki hankulan jama’a a ciki da wajen ƙasar nan.
You must be logged in to post a comment Login