Kiwon Lafiya
Gwamnatin Kano za ta fara hukunta duk ma’aikacin lafiyar da baya sa kayan aikinsa a Asibiti- Nagoda

Gwamnatin jihar Kano ta ce daga karshen watan Maris mai kamawa za ta fara hukunta duk wani jami’in lafiyar da aka samu bai sanya kayansa na aiki ba a cikin Asibiti.
Babban sakataren hukumar kula da Asibitocin jihar Dakta Mansur Mudi Na Goda ne ya bayyana hakan lokacin da yake rabon kayan sawar ga shugababnin kowanne bangaren ma’aikata na Asibitocin wato Daraktoci.
Ya kuma ce hakan na cikin kokarin da gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ke yi na tsaftace fannin kula da Lafiya.
Hukumar ta Hospital Management Board dai ta gudanar da rabon kayan sawar kyauta ga ma’aikatan lafiyar da gwamnatin jihar Kano ta samar a yau Asabar 22 ga watan Fabrairun shekarar 2025.
Ta cikin wata sanarwa da jami’ar hurda da jama’a ta hukumar kula da Asibitocin Hajiya Samira Sulaima ta ce, ma’aikatar ta gargadi ma’aikata da su rinkayin shiga mai dauke da cikakkun kayyakin su na aiki.
A cewar sanarwar gwamnatin ta amince a baiwa kowanne ma’aikaci yadi hudu na kayan da yake aiki dashi da zai isheshi.
Kazalika sanarwar ta ce za a fara rabawa ma’aikatan lafiyar kayan da suke aikin dan dinkawa daga gobe Litinin 23 ga watan Fabrairun shekarar ta 2025.
Haka kuma an baiwa kowanne ma’aikaci adadin wata daya da ya tabbatar da ya dinka kayan nasa.
Babban sakataren hukumar kula da Asibitocin Dakta Nagoda ya kuma gargadi duk ma’aikacin da aka samu ya sayar da kayan da aka bashi kan ya kuka da kansa.
You must be logged in to post a comment Login