Labaran Kano
Gwamnatin Kano za ta yi rigakafi ga yara sama da miliyan 3
Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta ci gaba da yakar cutar shan inna wato Polio, kasancewar cuta ce da ta ke taba laka tare da haifar da shanyewar wani bangare na jikin kananan yara a cikin kankanin lokaci.
Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana hakan yau a wani taron manema labarai da ya mayar da hankali a kan gangamin rigakafin cutar ta shan’inna da za a gudanar a kananan hukumomi 44 da ke nan jihar Kano.
Dakta Tsanyawa ya kuma kara da jan hankalin iyaye wajen baiwa jam’ian lafiya dake zagayawa gida-gida hadin kai domin yi wa yaransu allurar rigakafin domin hada hannu wajen yakar cutar.
Ya kuma ce a halin yanzu ma’aikatar ta karbi allurai fiye da miliyyan uku da dubu dari shida daga hukumar bunkasa lafiya ta kasa a matakin farko, inda ake sa ran yi wa yara miliyan uku da dubu dari biyu da arba’in da biyu da arba’in allurar, wadanda suke tsakanin watanni 59, inda kuma tuni aka baiwa ma’aikata dubu talatin horo a kan aikin.
Wakiliyarmu Zahra’u Nasir ta ruwaito cewa kwamishinan ya ce tuni ma’aikatar lafiya ta dauki matakan kariya cikin gaggawa domin hana cutar nan ta Corona Virus shigowa jihar Kano.