Labarai
Gwamnatin Kano zata kawo karshen barazanar yajin aikin ma’aikata
Gwamnatin jihar Kano ta kafa wani kwamiti na musamman wanda zai sasanta tsakaninta da gamayyar kungiyoyin kwadago na jihar wadanda suka bata wa’adin makwanni biyu kan ko dai ta mai dowawa da ma’aikatan jihar kudaden albashinsu da ta rage ko kuma ta tsunduma yajin aiki.
Shugaban gamayyar kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar Kano, Kwamared Kabiru Ado Minjibir ne ya bayyana haka, ta cikin shirin ‘Muleka Mugano’ na nan tashar freedom Rediyo da ya gudana a daren jiya.
Ya ce, kwamitin yana karkashin jagorancin sakataren Gwamnatin jihar Kano ne, Alhaji Usman Alhaji.
NLC da wasu kungiyoyi sun shawarci gwamnati kan kudaden Paris Club
NLC:sunyi barazanar tsunduma yajin aikin gama gari
Kwamared Kabiru Ado Munjibir ya kuma ce, tun a ranar juma’a da ta gabata ne suka fara tattaunawa da ‘yan kwamitin domin samar da mafita game da batun rage albashin ma’aikatan a watan da ya gabata.
A ranar larabar da ta gabata ne bayan wani taron gaggawa da gamayyar kungiyoyin kwadagon suka gabatar, suka bayyana rashin jin dadinsu kan matakin da gwamnati ta dauka na ragewa ma’aikata albashi.
You must be logged in to post a comment Login